Za a fara gurfanar da ‘yan Boko Haram da aka kama a Kotu

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ranar 9 Ga Oktoba ne za a fara shari’ar mutane sama da 1600, wadanda ake zargi da aikata ayyukan Boko Haram.

An dakatar da shari’un wasu dimbin ‘yan Boko Haram a cikin Yuli, saboda hutun da Alkalai su ka tafi.

Amma a ranar Lahadi, Ministan Shari’a Abubakar Malami ya bayyana za a ci gaba da wadannan shari’a.

Kakakin yada labaran ministan ne, Salihu Isa ya bayyana cewa za a ci gaba da sauran shari’un na wadanda ake tsare da su a gidajen kurkuku daban daban na kasar nan.

“Za a fara shari’ar 1600 da ake tsare da su a Kainji a ranar 9 Ga Oktoba, kuma an ware wasu alkalai hudu wadanda wani Babban Jojin Babbar Kotun Tarayya zai taya yi musu shari’a.”

Da zaran an fara wannan, za a fara shari’ar wadanda ke tsare a Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri. Duk wadannan inji shi, idan an fara babu jan lokaci za a kammala.

Sanarwar ta kara da cewa an zartas da hukunci akan wasu ‘yan Boko Haram su 9.

“Akwai wasu 220 wadanda ke tsare, amma an yarda cewa za a sake su, a yi musu wankan tsarkin mayar da su cikin al’umma nagari. Hakan ya kasance ne, sakamakon babu wasu kwararan shaidu a kan su.”

“Akwai wasu 651, wadanda ke tsare a Barikin Giwa na Maiduguri, Babbar Kotun Tarayya ta Maiduguri ce ta ce a ci gaba da ajiyar su a can.”

Binciken da aka gudanar a kan sama da 1600 da ke tsare a Barikin Sojoji na Wawa, Kainji da ke cikin Karamar Hukumar New Bussa ta Jihar Neja, wanda jami’an sojoji da sauran hukumomin tsaro su ka yi, ya nuna cewa akwai kalubale dangane da shari’un su.

“Wasu matsalolin da ke tattare da shari’ar ‘yan Boko Haram, sun hada da:

Rashin kwakkwaran bayanan bincike; yawan dogaro da furucin wanda aka kama da laifin aikata ta’addanci, rashin kwararan hujjoji na gwaje-gwaje da aune-aune, da kuma rashin hadin kai tsakanin masu bincike da masu gabatar da kara kafin a fara binciken.

Share.

game da Author