UBANGIDA: Zamanin sai wane ko dan wane za a dauka aiki ya wuce a Najeriya – Lai Mohammed

1

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed ya bayyana cewa zamanin sai wane ko dan wane za a dauka aiki a ma’aikatun Najeriya ya wuce, ko ma a wane irin mataki ko matsayi ne.

Ministan ya yi wannan jawabi ne a Abuja, ranar Lahadi a wuri taron godiya ga Mahalicci da sabuwar Babbar Sakatare ta Ma’aikatar Yada Labarai, Grace Gekpe ta shirya.

Manajan Darakta na Kamfanin Dillanci Labarai, NAN ne, Bayo Onanuga ya wakilci Ministan, inda ya ce duk wani mukami da gwamnatin tarayya za ta nada, ta na yi ne a kan cancanta, nagarta da kwarewa.

“Ai yanzu an daina turo wani ko wata daga sama don a bashi mukami. Wannan ba sigogin wannan gwamnati ba ne. Zai yi kyau na tuna muku cewa gwamnati ta shirya wa manema mukaman Babban Sakatare jarabawa kafin a dauke su. To Gekpe ta na cikin wadanda su ka zauna wannan jarabawa, kuma ta ci.”

Lai ya ce akwai bukatar kara wa hukumomin da ke karkashin ma’aikatar sa kudade daga gwamnati. Ya kuma yi bayanin cewa gwamnati mai ci yanzu ta na gudanar da ayyukan raya kasa masu dimbin yawa, amma ‘yan adawa ne ke kururuta cewa ba a komai.

Daga nai sai ya ce akwai kuma bukatar gwamnati ta yi amfani da kwararrun masu wayar da kai ta hanyar yada bayanai, domin su kara sanarwa da bayyana wa al’umma irin wannan dimbin ayyuka da gwamnati ke yi.

Share.

game da Author