ZAZZABI: Maganin ‘Artesunate’ ba ya Illar da ake zaton yana yi a jiki

0

Hukumar kula da abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta ce rashin fahimta ce ya sa aka hana amfani da wasu magungunar warkar da cutar zazzabin cizon sauro 42.

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne Majalisar dattawa ta umarci kwamitin ta na Kiwon Lafiya da ta gudanar da bincike kan wasu magungunar cutar zazzabin cizon Sauron 42 da bai kamata ace ana siyar da su a kasuwannin kasarnan ba saboda illar da suke dashi kamar yadda kungiyar kasashen turai EU ta sanar a kwanakin baya.

Kungiyar kasashen turai EU ta hana amfani da wannan magunguanan ne domin illar da ya ke yi wa kodar mutane masu amfani da su.

Makaddashin hukumar NAFDAC Yetunde Oni ta ce magungunar da aka hana amfani da su kamar su ‘Artesunate’ bai kamata ana shan su zallaba sai an gaurayasu da wani magani kafin a yi amfani da su.

Ta ce bai kamata ana amfani da wadannan magunguna ba musamman domin samun sauki da ga cutar maleriya domin suna da matukar illa a jikin mutum.

Yetunde Oni ta ce magunguna kamar su ‘temisin Combination Therapies (ACTs)’ wanda hukumar WHO ta amince da su ne ya kamata a yi amfani da su idan ana fama da zazzabi cizon sauro.

Daga karshe ta shawarci mutane da su tabbatar da ingancin magungunan da za su siya ta hanyar duba kwanaki da watan da zai daina aiki.

Ta kuma ce hukumar su ta bada wasu lambobi da mutanen za su iya aikawa da lambar dake jikin kwalin magani wanda hakan zai taimaka wajen tabbatar da ingancin maganin.

Share.

game da Author