Wata dalibar kwalejin koyar da aikin malunta dake garin Pankshin jihar Filato ta rasa wajen zubar da ciki da take dauke dashi.
Kamfanin dilancin labaran Najeriya ta ruwaito cewa makwabtan dalibar ne suka gano cewa akwai matsala bayan rashin ganin wulkawarta a ranar ranar Litini kamar yadda ta saba.
Ko da makwabtan suka leka dakin ta tagan dakin sai suka hango ta a kwance kamar babu rai a jikinta.
Nan da nan sai makwabtan suka kira ‘yan sanda da ga nan ne fa bayan bincike a gano cewa lallai babu rai a jikinta.
Sai da aka balla kofar dakin nata kafin a shiga.
Jami’in harka da jama’a na rundunar ‘yan sandar jihar Filato Tyopev Terna ya ce sun kai dalibar babbar asibitin Panshin inda likita ya tabbatar musu cewa dalilin zubar da cikin da ta ke dauki da shine yayi sanadiyyar rasuwar Nenfort Ezekiel.
Ya ce sun fara gudanar da bincike bisa ga dalilan da ka iya kawo ajalinta wanda likita ya fada amma babu wanda suka kama.
Ya ce ko ba don komai ba za su so gudanar da bincike don gano wanda ya yi wa dalibar ciki.
Jami’in kula da harka da jama’a na kwalejin Istifanus Kyakmut ya yi kira ga sauran daliban makarantan da su mai da hankalinsu kan karatunsu.
Iyalen mamaciyar su dauki gwar domin a yi mata jan’iza a kauyen Kanke.