A wata zama da kungiyar ‘yan jarida ta kasa tayi a Abuja ranar Alhamis ta gargadi gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da ya daina muzguna wa ‘yan jarida da ya keyi a jihar Kaduna.
Sakataren kungiyar Shuaibu Leman ya ce ba za su sa ido su bari gwamnan na yin amfani da kujerarsa wajen muzguna wa ‘yan jarida a jihar.
Kungiyar ta fitar da wannan sanarwa ne bayan zaman da kotu tayi na sauraren karar da gwamnan El-Rufai ya shigar kan wani rahoto da Binniyat tsohon ma’aikacin gidan jaridar Vanguard ya rubuta na karya kan jihar.
Duk da cewa Binniyat ya halarci kotun a halin rashin lafiya inda ba ya iya tafiya sai da sanda amma alkalin kotu ya yanke hukunci a daure shi har sai ranar 20 ga wannan watan.
NUJ ta gargadi gwamna El-Rufai cewa shine zasu nema idan har wani abu ya sami Binniyat.
Da aka nemi ji ta bakin kakakin gwamnan El-Rufai, Samuel Aruwan ya citura domin bai amsa wayoyinsa ba.
Discussion about this post