Wata likitan kula da yara kanana kuma ma’aikaciyar babbar asibitin jami’ar Ibadan Olukemi Tango ta jaddada mahimmancin shayar da yara nonon uwa da zaran an haife su sannan kuma da mahimmancin ci gaba da hakan har na dan wani lokaci kafin a yayeshi domin gujewa matsalolin da ka iya tasowa da zai iya sa a rasa ran da.
Ta fadi hakan ne a lokacin da kamfani dillancin labaran Najeriya da ita ranar Lahadi a Ibadan.
Olukemi Tongo mamba ce na kungiyan likitocin da ke kula da yara kanana NISOMN.
Likitan ta ce za a iya magance dalilan da ke kawo mutuwan yara kanana musamman wanda ya hada da matsalar bakwaini ( yaron da aka Haifa kafin ya cika wata tara), rashin kuka da nufasawan yaro bayan haihuwa da kuma sauran cututtuka ta hanyar wayar da kan uwayen yaran da kuma ma’aikatan jinya’’.
Daga karshe Olukemi ta ce kungiyar su ta NISOMN za ta shirya taron wayar da kan mutane musamman mata da ma’aikatan jinya kan yadda za su kula da yara kanana domin guje wa kamuwa da cututtukan da ke hallaka yara.
Za a gudanar da irin wannan taro ne ranar hudu ga watan Yuli a garin Ibadan, jihar Oyo.