Gwamnatocin kasashen Saudiyya Arabiya, Bahrain, Hadaddiyar Daular Larabawa UAE, da kuma Masar, sun sanar da yanke Duk wata alaka da suke dashi da kasar Qatar.
Gwamnatocin kasashen sun sanar cewa sun yi haka ne bisa zargi da suke wa kasar Qatar din da marawa kungiyoyin ‘yan ta’adda wadanda suke barazana ga Saudiyya da kuma sauran kasashen larabawa na yankin.
Bayan haka kasar Saudiyya ta sanar da cire kasar Qatar daga kungiyar kawancen kasashen larabawa da ke yaki da ‘yan tsagerun a kasar Yemen, wanda Saudiyya ta kafa kuma jagorantarsa.
Dalilin wannan mamaki da kasashen suka dauka, sun kuma dakatar da dukkanin tafiye-tafiye na jiragen sama da kasa da kuma ta ruwa daga kasashensu zuwa kasar na Qatar.
Discussion about this post