Dalung Ya Ragargaji Sheikh Pantami don ya yi masa tayin addinin Musulunci

1

Ministan Wasanni Solomon Dalung, ya soki lamirin hanyar da Sheikh Isa Pantami ya bi inda ya yi kiran sa da ya shiga addinin Musulunci. A makon jiya ne dai ministan ya kai ziyara a Masallacin Annur, a Abuja inda Pantami ke gabatar da Tafsir cikin watan azumi.

Dalung ya ce a gaskiya Shehin malamin ya tozarta shi da ya gayyace shi cewa ya shiga musulunci. Ya yi korafin cewa shekara biyar kenan ya na zuwa tafsir a masallatai daban-daban, domin karfafa dangantaka tsakanin addinai biyu.

“Inda a ce da zuciya daya Pantami ya yi min kiran, me ya sa tun can baya bai taba yi min kiran ba, sai da na ziyarce shi?”

Dalung

Cikin sanarwar da ministan ya fitar, kuma Shugaban Ma’aikatansa Maiwada Danmalam ya watsa, Dalung ya ce ya yi mamakin yadda Pantami ya ki yin koyi da Annabi SAW, wanda da tawagar Kiristoci su ka gayyace shi daga Sinai, ya karbe su hannu biyu, kuma har ya bar musu masallaci suka yi ibadar su a ciki.

A karshe ya yi muni da cewa zamantakewa na iya yiwuwa tsakanin mabambata addinai, dalili kenan ma ya sa ya ke yawon ziyartar musulmi domin karfafa wannan zumunci.

“Irin yadda ya yi min wannan kira gatse-gatse, ai kawaici na nuna a lokacin na nuna kamar ban damu ba. Me ya hana ya same ni ofis ya yi min wannan kiran. Ina mu’amalar ziyara ga Shekh Dahiru Bauchi da Sheikh Bala Lau, amma ba su taba yi min irin haka ba.”

Sannan kuma na yi mamakin yadda bayan ziyarar da na kai, sai aka yi ta yadawa cewa na karbi addinin musulunci. Shin wa ya gaya musu a rannan ne na fara shiga masallatai?”

Dalung Solomon

Share.

game da Author