KIWON LAFIYA: Nasarori da Matsalolin da aka fuskanta shekaru biyu bayan rantsar da gwamnati Buhari

0

Tun da aka rantsar da sabuwar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ne masu yin tsokaci akan fannin kiwon lafiya suka dau alkalummarsu domin yin sharhi akan yadda gwamnatin ta ke gudanar da al’amurranta musamman a fanni kiwon lafiya a kasar.

Masu sharhi sun yi rubuce-rubuce na ra’ayoyi da yin bita akan abubuwan da ke gudana a wannan fanni a kafafen yada labarai da dai sauransu.

Ko da yake da yawa daga cikin wadannan tsokaci na da nasaba ne da irin yadda wadansu cututtuka da suka kusa fin karfin ma’aikatar kiwon lafiyar kasar da kuma rashin maida hankali da ba’ayi ba don ganin ire-iren hakan bai dagula lissafi ko shirye-shiryen gwamnati a fannin kiwon lafiyar mutanen kasar ba.

Kamar yadda gwamnati da dauki alkawura a lokacin yakin neman zabe, mun bi sashe -sashe na fannin domin ganin ko ina ka kwana zuwa yanzu.

GYARA CIBIYOYIN KIWON LAFIYA NA MATAKIN FARKO

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya ce tun bayan rantsar da wannan gwamnati, aka samar da kudade domin gyara cibiyoyin kiwon lafiyar da ya kai 10,000 wanda ya hada da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a fadin kasa Najeriya.

Tuni har an fara dibar romon hakan domin yanzu haka wasu cibiyoyi sun fara shaida wannan aiki na gwamnatin tarayya kamar asibitin Kuchigoro daka babban birnin tarayya, Abuja.

Duk da cewa an samu irin wannan cigaba, har yanzu akwai rashin samun kula da wasu da yawa daga cikin asibitocin kasar da ke neman a waiwaye su.

CUTAR SANKARAU

Tun a watan Nuwambar 2016 ne cutar Sankarau ta fara yaduwa a fadin kasar nan inda bayanai suka nuna cewa mutane 1114 ne suka rasa yarukansu a sanadiyyar cutar a fadin kasarnan.

Hukumar kula da hana yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta sanar da cewa adadin yawan mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyyar kamuwa da cutar sankarau ya kai 1069 sannan kuma mutane 13,420 na dauke da cutar a jihohi 23 a Najeriya
Hukumar ta sanar da hakan ne ranar takwas ga watan Mayu inda ta cewa an gwada jinin mutane 897 sannan kuma sakamakon gwajin da akayi ya nuna cewa mutane 448 daga cikin su na dauke da cutar.

Cibiyar ta kuma kara da cewa daga cikin mutane 13,420 wadanda suke dauke da cutar 5,724 yara ne masu shekaru 5 zuwa 14.
meningitis patient

A yanzu haka bincike ya nuna cewa kananan hukumomi 48 a jihohin kasa Najeriya da ya hada da Zamfara, Sokoto,Kano Katsina,Kebbi da Yobe suka fi fama da cutar sankarau din.

Daga karshe hukumar ta ce gwamnatin Najeriya ta tura ma’aikatan kiwon lafiya domin kulawa da mutanen da suka kamu da cutar ranar Asabar shida ga watan Mayu zuwa jihohin Zamfara da Sokoto sannan kuma jihar Zamfara za ta sami Karin alluran rigakafin daya kai 694,065.

CUTAR SHAN INNA

Bayan dimbin gudunmuwar da gwamnatin Najeriya tayi ta samu domin kawar da cutar shan-Inna a kasar, hankalin masana da masu yin fashin baki akan abubuwan da ya shafi yaduwar wannan cuta na San-Inna ya tashi ganin yadda cutar ta nemi ta dawo a wasu sassan kasar nan.

Hakan kuma yana da nasaba ne da yake-yaken da akayi ta fama dashi a jihohin Barno, Yobe da Adamawa, da wasu sassan Arewa maso-gabas.

Najeriya na gab da ta karbi shaida fatattakar cutar a watan Mayun bana sai kuma aka sake samun burbudin cutar a wasu sassan jihar Barno din.

Yanzu ma’aikatar Lafiya ta sake karkata akalarta zuwa wadannan yankuna domin ganin an kawar da shi kwata-kwata wannan karon.

AGAJI DA TAIMAKO

Bayanai sun nuna cewa mafi yawa-yawa daga cikin kudaden da ake amfani dasu wajen kau da cututtuka a kasa Najeriya sukan samu ne ta hanyar Agaji da Taimako da ake ba kasar.

Najeriya ta more irin wadannan taimako daga kungiyoyin majalisar dinkin duniya da na kasashen da suka ci gaba da wadansu masu zaman kansu.

Hakan yasa sau da yawa gwamnati na iya tunkarar matsalolin bullowar cututtuka a kasar cikin gaggawa.

KARANCIN MA’AIKATAN ASIBITI.

Shugaban kungiyar likitocin Najeriya Mike Ogirima ya ce babbar matsalar da asibitocin kasarnan ke fama da shi shine na rashin kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya.

A watan da ya gabata ne gwamnatin jhar Gombe ta dakatar da sallamar wadansu ma’aikatan kiwon lafiya masu yawa da ya hada da unguwanzoma 100 saboda babu wadanda zasu maye gurbinsu.

Bayan haka ana fama da karancin kayayyakin aiki a asibitocin kasar nan.

ALBASHIN MA’AIKATAN KIWON LAFIYA

Yajin aiki da likitoci suke yi a fadin kasarnan na ci ma gwamnati tuwo a kwarya musamman ganin cewa hakan yakan shafi marasa lafiya wanda wasu ma suna kwance ne a asibitocin a lokacin da hakan yake faruwa.

Irin hakan yana da nasaba ne da rashin biyan malamai da ma’aikatan asibitocin kasarnan Albashinsu akan lokaci da alawus dinsu da ya kamata.

Da ga baya baya bayannan ma sai da Kungiyar likitocin Najeriya ta gargadi gwamanti da ta dakatar da wani shiri da take yi na maida albashin likitoci tare da na ma’aikatan jinya da unguwan zoma bai daya.

Shima wannan ya zamo babbar matsala ga fannin kiwon lafiyar kasa musamman a wannan lokaci.

Share.

game da Author