Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya yi kira ga yan Najeriya da su ci gaba da yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a.
Bayan haka Osinbajo ya yi bayanin kan nasarorin da wannan gwamnati ta samu a bisa jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari, a cikin shekaru biyu.
Osinbajo ya yi bayanin ne a cikin wani dogon jawabi da ya gabatar wa al’ummar Najeriya a ranar bikin tuna ranar Demokradiyya.
A cikin jawabin, Osinbajo ya bayyana fannonin da aka samu ci gaba, musammam wajen yaki da cin hanci da rashawa, dakile karfin Boko Haram da sauran nau’o’in ta’addanci, shirye-shiryen samar wa matasa abin dogaro ta hanyar shirin N-Power da kuma shirin ciyarwa ga ‘yan makaranta.
“Gwamnatin mu ta ware wasu muhimman fannoni uku, wadanda ta yi wa tallafa ta gaggawa tun farkon hawan mu. Wadannan fannoni sun hada da matsalar tsaro, cin hanci da rashawa da kuma matsalar tattalin arziki” Inji Mukaddashi Osinbajo.
Sai dai kuma duk da wadannan nasarori da ya bayyana, ya ce gwamnarin su ta ci karo da kalubale, musamman a fannin tattalin arziki.
“Na yarda da dcewa matsalar tattalin arziki ita ce babbar matsalar da ta zarce kowace a kasar nan. Bari na yi amfani da wannan dama na bayyana muku irin damuwar mu dangane da wannan matsala.
Osinbajo ya kuma roki’yan Najeriya su ci gaba da yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’ar kara samun sauki. Buhari dai na Ingila ya na hutu inda ake kara duba lafiyar sa.