Hukumar kula da hana yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta sanar da cewa adadin yawan mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyyar kamuwa da cutar sankarau ya kai 1069 sannan kuma mutane 13,420 na dauke da cutar a jihohi 23 a Najeriya
Hukumar ta sanar da hakan ne ranar takwas ga watan Mayu inda ta cewa an gwada jinin mutane 897 sannan kuma sakamakon gwajin da akayi ya nuna cewa mutane 448 daga cikin su na dauke da cutar.
Cibiyar ta kuma kara da cewa daga cikin mutane 13,420 wadanda suke dauke da cutar 5,724 yara ne masu shekaru 5 zuwa 14.
A yanzu haka bincike ya nuna cewa kananan hukumomi 48 a jihohin kasa Najeriya da ya hada da Zamfara, Sokoto,Kano Katsina,Kebbi da Yobe suka fi fama da cutar sankarau din.
Daga karshe hukumar ta ce gwamnatin Najeriya ta tura ma’aikatan kiwon lafiya domin kulawa da mutanen da suka kamu da cutar ranar Asabar shida ga watan Mayu zuwa jihohin Zamfara da Sokoto sannan kuma jihar Zamfara za ta sami Karin alluran rigakafin daya kai 694,065.