Kotu a Kaduna ta gargadi gwamnatin Jihar Kaduna da kada ta kuskura ta ci gaba da shirinta na rusa Kasuwar Barci dake Tudun Wada Kaduna.
Alkalin Kotun Mohammed Bello ya ce kotu ta yanke hukuncin haka ne ganin cewa akwai wasu batutuwa da ake ta takaddama akai na dalilan da zai sa dole sai ya rusa Kasuwar dake gaban Kotun.
Kotu ta ce gwamnati ta dakata tukuna har sai ta yanke hukuncin ko ta na da ikon rusa kasuwar da mutane ke gudanar da kasuwancin su ko a a.
Wasu ‘yan kasuwan ne suka shigar da karar inda suke kalubalantar geamnatin Jihar kan shirinta na rusa kasuwar.
Hankalin ‘yan Kasuwar Barci ya tashi tun lokacin da gwamnatin Jihar ta sanar da shirin rusa Kasuwar.
Yanzu dai an daga ci gaba da sauraron karan zuwa ranar 5 ga watan Yuni.