Sakatare janar na kungiyar kula da harkokin addinin Musulunci NSCIA Ishaq Oloyede ne ya sanar da haka.
Yace Sarkin Musulmi Abubakar zai sanar
Da manema labarai da jama’ar kasa a daren yau.
Gobe Asabar Musulman kasa Najeriya zasu tashi da Azumi.
Sanarwan ya nuna cewa an ga watan a jihohi da dama a kasar.