Wani dan kwallon kungiyar kwallon kafa na Kwara United Saka Azeez ya yanke jiki ya fadi yau a filin wasa na Ilori a daidai suna gudun motsa jiki a shirin wasan kwallon kafa da su keyi na Kwararru wato ‘Premier League’.
Mahaifinsa Kasali Lasisi shahararren dan wasan kwallon Tabur ne ‘Table Tennis’ wanda gwamnatin jihar Kwara ta karrama a kwanakin nan.
Kakakin kungiyar kwallon kafan yace abin ya basu tsoro domin suna gudun motsa jiki ne kawai sai ya yanke jiki ya fadi.
“ Da yake muna kusa da asibiti ne sai muka dauke shi ranga-ranga zuwa can. Bayan likitoci sun duba shi sai suka sanar mana cewa ya riga ya cika.”
Kungiyar kwallon kafa na Kwara United sun siya Azeez ne daga Zamfara United a farkon wannan shekarar kwallo wato 2017/2018.