Maniyyatan jihar Kaduna zasu biya Naira Miliyan 1.5 a matsayin kudin Haji bana.
Jami’in dake kula da hudda da jama’a na hukumar Alhazai na jihar Kaduna Abdullahi Yunusa ne ya sanar da haka a Kaduna.
Yace hukumar kula da aikin Haji ta kasa ne ta sanar masu haka a wata wasika da ya ke bada bayanai akan yadda aka kasafta kudaden da abin da kowani maniyyaci zai biya.
Yace za a ba kowani mahajjaci Dala 800 a matsayin kudin guziri.
Daga karshe Yunusa yayi kira ga maniyyata da su hanzarta cikata kudaden su Kafin lokaci ya kure.