Tun ana ta cewa abin da kamar wuya yanzu dai gashi a zahiri domin mutanen Zariya sun yi buda bakin azumin bana kuma na farko da ruwan famfo na zuba shaaaa.
Duk wani mazaunin garin Zariya ya kusan cire rai akan samun ruwan famfo a nan kusa sai gashi gwamnati mai ci wato gwamnatin El-Rufai ta ce za ta iya kuma tayi.
Yau Asabar ne aka kaddamar da kammala aikin wadata garin Zariya da ruwan famfo wanda wasu su kance an shekara sama da 20 babu ruwan famfo a garin.
El-Rufai ya kaddamar da hakan a wata gajeruwar buki da akayi a Zariya.
Sashen da aka gama kuma aka kaddamar Yau zai wadata garin Zariya da ruwa da ya kai lita Miliyan 150 a kullum.
Gwamnan jihar ya yabi wa kwamishinan ruwan jihar Suleiman Aliyu Lere kan tsayawa tsayin daka da yayi domin ganin abinda gwamnati ta sa a gaba na samun nasara akan aikin ruwan Zariya ya yiwu.
Mutanen Zariya da suka tattauna da gidan jaridar Premium Times Hausa sun jinjina wa gwamna El-Rufai kan ganin wannan aiki ya tabbata a zamanin mulkinsa.
” Wannan abin farincikin da ya same mu ba za mu ta ba mantawa da shi ba. Ni dai na shekara 40 amma gaskiya Duk da ba zama nakeyi ba a garin amma ban taba ganin ruwan famfo a Zariya ba in ba na rijiyar burtsate ba amma wai ka bude famfo ka ga ruwa sai dai kila daga yanzu.Mu fa El-Rufai yayi mana komai.” Inji Umar Mohammed
Gwamna El-Rufai ya ce gwamnati zata ci gaba da aiki a sashen matatar ruwar na biyu.
Bayan haka ya zazzagaya wasu kananan hukumomin jihar domin duba ayyukan da gwamnati ta keyi a garuruwan.