Jaruma mai tasowa Samira Saje ta tattauna da Premium Times Hausa, sati uku bayan rasuwar mahaifiyar ta a watan Maris, 2017.
Mahaifin ta ya rasu shekara uku da suka wuce.
A wannan tattaunawa za a ji asalin ta, yadda ta shaku da iyayen na ta da kuma halin da jarumar ke ciki yanzu da ta ke karatun digiri na farko a Jami’ar Alqalam da ke Katsina.
PT: Samira mu na kara yi miki ta’aziyyar rashin mahaifiyar ki.
Samira: Na gode kwarai Allah ya saka da alheri.
PT: Ganin yadda ki ke yawan tura hotunan ki tare da mahaifiyar ki a shafukan ki na Facebook da Instagram, shin wace irin shakuwa ku ka yi ne kafin rasuwar ta.
Samira: Mahaifiya ta ta fi kowa kusanci da ni, mun zama tamkar kawayen juna. Na dade da daina kwana daki na, ina kwana dakin ta kuma a kan gado daya mu ke kwana har rasuwar ta.
PT: Lallai kun shaku sosai.
Samira: Ka san ita ma’aikaciyar banki ce a Kaduna, amma da aka yi mata canjin aiki zuwa Kano, sai mu ka dawo Kano, inda a nan Kano din ta rasu.
Gaskiya na yi babban rashi, kuma sai yanzu na san ciwon rashin iyaye. Saboda rasuwar mahaifiya ta na gigita matuka. Na rasa mahaifi cikin 2014, yanzu na rasa mahaifiya. Yanzu ni marainiya ce gaba da baya.
Idan ina barci har tashi ta kan yi cikin dare ta na kallo na, ta ga shin ko akwai wani abu da ke damu na wanda ban fada mata ba?
PT: Rashin lafiya ta yi ko hadari?
Samira: Ba hadari ta yi ba, rashin lafiya ce, ka san idan ajali ya yi kira, kuma kwana ya kare, to an zo kan iyakar rayuwa kenan.
PT: Ku ‘yan asalin ina ne?
Samira: Sunan mahaifi na Alhaji Sulaiman Adam Saje. Ya rasu ya na da shekaru 73 a duniya. Mahaifiya ta kuma Hajiya A’ishatu Machima Abubakar.
PT: Saje ne na soja ko saje na dan sanda, ko saje ake nufi na gashin fuska?
Samira: A’a, sarauta ce. Kaka na shi ne Sarkin garin Dambazzau a Karamar Hukumar Gassol cikin Jihar Taraba. To ni kuma sai aka nada mahaifina sarautar Saje na garin Marabar Gassol.
PT: Yanzu wane hali ki ke ciki?
Samira: Ina cikin halin maraici. Ka san kuma bayan na gama karatun Diploma a Kaduna Polytechnic, yanzu na samu shiga Jami’ar Alqalam University a Katsina. Yanzu haka ina Katsina. Kuma idan na ce maka ina cikin halin maraici, na tabbata za ka yarda da ni, tunda dai ka san halin na, ka san ni kowace ce.
PT: Yanzu kin ja baya da harkar fina-finai kenan?
Samira: Zan iya cewa a yanzu na dan ja baya. Na farko ga jimamin rashin mahaifiya. Na biyu kuma ga karatu a Katsina, ba a Kano ko Kaduna ba.
PT: Wane kwas ki ke yi ne?
Samira: Ina kwas din aikin banki, dama a kan sa na yi diploma.
PT: Ina batun harkar tallar kayan kwalisa da ki ke yi wanda ku ke saka suturu ku na tafiya a gaban ‘yan kallo, wato tafiyar-kasaitattar-mage?
Samira: E, ina yi ban daina ba. Ka san na yi wa kamfanoni talla da suka hada da: Tozali Magazine, Zeenat Couture na Abuja da KDC Fashion.
PT: Yanzu mene ne fatan ki?
Samira: Ni yanzu ba ni da sauran jin dadi kuma. Yaya na daya kadai ya rage, sai ni. Fata na Allah ya ba ni mijin da muka dace da juna, na yi aure kafin na kammala digiri.