Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi suka da kakkausar murya kan harin da aka kai kauyen Asso dake kudancin Kaduna.
El-Rufai ya mika Jajen sa ne ga mutanen kauyen da aka kai ma wannan mummunar hari a wata sanarwa da kakakin gwamna Samuel Aruwan ya sanya wa hannu.
Bayan haka kuma ya sanar da kafa wata sabuwar rundunar jami’an soji da akayi wa suna ” Operation Harbin Kananan” kuma zata fara aiki a yankin kudancin Kaduna na ba da dadewa ba.
Duk da cewa ba a sanar da yawan mutanen da suka rasa rayukansu a sanadiyyar harin ba, rikici irin wannan ba farau ba a yankin kudancin Kaduna inda bayanai da suka fito wa wancan lokacin ya nuna cewa akalla mutane 200 ne suka rasa rayukansu a ire-iren wadannan hare-hare.
El-Rufai ya ce gwannati zata yi duk abin da ya kamata domin ganin an fatattaki irin wadannan ‘yan ta’adda a dazukan yankin.