Hukumar kiwon lafiya ta duniya wato ‘WHO’ ta sanar da cewa kamfanin GlaxoSmithKline (GSK) na kasar Britaniya ta sarrafa wata sabuwar allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro mai suna “Mosquirix”.
Hukumar ta ce a sakamakon haka za ta gwada ingancin maganin a shekaran 2018 akan musamman yara kanana daga shekara biyar zuwa kasa a kasashen da suka fi kamuwa da cutar Zazzabin cizan sauron.
Kasashen kuwa sun hada da Ghana, Kenya da Malawi.
Wani jami’in hukumar mai suna Matshidiso Moeti yace dalilin da ya sa kungiyar ta shirya yin hakan shine don jarraba ingancin maganin kafin a baza shi a sauran kashen duniya da ke bukatar irin wannan taimako.
Ya ce bincike ya nuna cewa duk shekara a kasashen kudu da Saharan Afrika, akan rasa rayukan mutane sama 400,000 wanda mafiya yawan su yara kanana ne da kuma jirajirai duk a sanadiyyar zazzabin cizan sauro.
Moeti ya ce maganin zai taimaka wajen ceto rayukan mutane da dama a kasashen Afirka din.
Daga karshe hukumar WHO ta sanar da cewa sun sami kudaden da suke bukata na siyo alluran rigakafin cutar tun a watan Nuwamban bara.
” Mun sami kudaden ne daga tallafin da gidauniyar Bill da Melinda Gates suke badawa, asusun kawar da cutar kanjamau da tarin fuka ta duniya, asusun kula da alluran rigakafi ta duniya da wasu kungiyoyi masu kama da haka.