Masarautar Kano ta kare kanta dangane da zargin yin almubazzaranci da baitilmalin masarautar, inda ta fito karara ta ce ba gaskiya ba ne da aka ce ta kashe naira bilyan 6 cikin kasa da shekaru uku Na mulkin Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II.
Da ya ke wa manema labarai bayani a ranar Litinin, Walin Kano Alhaji Mahe Bashir Wali, ya ce Sarkin ya kashe naira bilyan 4.314, inda kuma Walin ya bayar da bayani dalla-dalla na yadda aka kashe kudaden.
Ya ce Sarki Sanusi ya zama Sarkin Kano cikin watan Yunin 2014, bayan rasuwar Sarkin Kano Ado Bayero.
Wannan bayanin ya zo ne kwanaki kadan bayan Hukumar Kai Kuka da Hana Cin Hanci da Rashawa ta jihar, ta ce za ta binciki zargin kashe kudade ba kan ka’ida ba da ake zargin Sarkin ya yi.
Walin Kano wanda shi ne mai kula da baitulmalin masarautar Kano, ya ce masarautar Na da kudi naira bilyan 2.8 a zamanin wancan sarki, har zuwa ranar 7 Ga Fabrairu, 2017, inda aka kashe naira milyan 981 a wani aiki na Bayero City Project a karkashin wancan Sarki kenan.
Wannan ya sa an rage naira bilyan 1.8 a bailtulmali.
“To wadannan adadi naira bilyan 1.8, shi ne abin da Sarki Muhammadu Sanusi II ya gada. Sabanin naira bilyan 4 da ake yayatawa.”
Wali ya ce daga cikin kudaden da aka kashe, akwai naira milyan 152 na sayen kayan kujeru da sauran kayayyakin da fada ke bukata, wadanda aka musanya bayan rasuwar Sarki Ado Bayero, domin dukkan kayan da ya mutu ya bari, an kwashe su an raba wa magadansa, kamar yadda shari’ar Musulunci ta ce a yi.”
“An kashe naira milyan 108 wa magadan Ado Bayero a matsayin kudin motocin da ya bari wanda Sarki Muhammadu Sanusi ya gada.” Wadannan motoci, Wali ya ce su na nan a cikin sauran bargar motocin da Fadar Masarautar Kano Ke da su.
Daga nan ya kara da cewa Masarautar ta sayo motoci biyu masu sulke a kan naira milyan 142, wadanda gwamnatin jihar Kano ce da kanta ta bayar da shawara da kuma amincewar a sayo motocin, saboda la’akari da mummunan harin da aka taba kai wa Sarki Ado Bayero.
Ya musanta cewa Masarautar ta sayo motocin alfarma guda biyu samfurin Rolls Royce domin amfanin Sarki Muhammadu Sanusi.
“Wadannan motoci fa abokan sa ne suka ba shi kyautar su.
Har ila yau, Wali ya ce daga watan Yuni 2014 zuwa Maris 2017, fadar Sarkin Kano ta karbi naira bilyan 1.7, wadanda ya ce a ka’idar dokar da ta kafa Masaurauta, ta 2004, ya kamata a ce nunki uku na wannan kudi ake karba.
” Abin da doka ta ce shi ne Masarauta ta karbi 3 bisa 100 na abin da ake ba kananan hukumomin Kano 44.”
Ya ce daga 2012 har zuwa yau an hana Masarautar Kano cikakken wannan kaso. Ya kuma ce tun bayan hawan Sarki Muhammadu Sanusi II ya kara yawan albashi da sauran alawus-alawus.
“Kafin hawan sa 2014, albashin naira milyan 9.910 ake biya. Daga hawansa kuma ake biyan naira milyan 39.” Wali ya ce gwamnatin jihar Kano na sane da wannan karin albashi.
Sarkin ya samu sabani ne da Gwamna Abdullahi Ganduje tun bayan jawabin da ya yi cewa rashin tunani ne a ciwo bashi daga kasar Chana a gina titin zirga-zirga jirgin kasa.
Bayan wannan kuma Sarkin ya soki katobarar da gwamnan jihar Zamfara ya yi cewa yawan zinace-zinace ya sa Allah ya yi fushi da al’ummar jihar ya saukar musu da ciwon sankarau.
Akwai kuma na jajircewar bayar da shawara kan karatun ilmin yara mata da ya yi sai kuma shirin sa na ka’ida da kawo dokoki da sharuddan yawan aure-aure.
Duk wadannan sun kawo masa tsangwama daga wasu ba’ari na jama’a.
Har ta kai gwamnan Zamfara ya ce shi ma Sarkin ai ba ya aikata abin da ya ke koyarwa.