Masarautar Kano ta musanta zargin da ake yi cewa Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya kashe Naira Bilyan 6 na baitulmalin masarautar daga hawan sa kan karagar mulki zuwa yanzu.
A wani taron manema labarai, babban Dan Majalisar Sarki mai lura da kudin baitulmalin Masarautar, wato Walin Kano, Bashir Wali, ya bayyana wa ‘yan jarida cewa masarautar ta kashe naira bilyan 2.9 ne kacal tun bayan hawan Sarki Muhammadu Sanusi II, cikin January, 2014.
Wali, wanda ya gabatar wa manema labarai da wasu takardun bayanan yadda aka kashe kudaden, y ace Sarki Sanusi ya gaji naira bilyan 1.9, ba naira bilyan 4 da ake ta yayatawa a wasu kafafen yada labarai ba.