Sifeton ‘yan sandan Najeriya Ibrahim Idris ya amince da aika karin jami’an ‘yan sanda zuwa yankin kudancin Kaduna domin shawo matsalar tsaro da ake ta fama da shi a yankin da yaki ci yaki cinyewa.
Kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Aghole Abeh ya fada wa manema labarai cewa shugaban ‘yan sandan Idris Ibrahim ya umurci jami’an ‘yan sandan da su hada da yin amfani da jiragen sama domin gudanar da shawagi a yankin ta sama domin gano maboyar masu tada zaune tsaye a yankin.
Bayan haka kuma Kwamishanan ‘yan sandan ya shawarci mutanen yankin da su ba jami’an tsaro hadin kai akan wannan aiki da suka sa a gaba.