Asusun tallafawa yara na majalisar dinkin duniya UNICEF, ta ce ta kashe kudaden daya kai naira biliyan 6.1 domin ciyar da yaran dake fama da yunwa a jihar Jigawa daga shekarar 2009 zuwa yanzu.
Wani jami’I a UNICEF din Abdulai Kaikai ne ya fadi hakan yayin da suka tattaunawa da masu ruwa da tsaki a jihar domin nemo hanyoyin da za’a bi don shawo kan matsalar yunwa a jihar.
Kaikai yace UNICEF wadatar da yara sama da 50,000 dake fama da yunwa a jihar da abinci sannan ta na kula da wadansu da suka kai 74,630 tun daga shekarar 2016.
Ya kuma ce hakan ya yiwu ne ta dalilin tallafin da suke samu daga wasu kungiyoyi masu zaman kansu da suka hada da ‘Department for International Development (DFID)’ da ‘Children Investment Fund Foundation (CIFF)’.
Bayan haka kuma wasu kungiyoyi a jihar na taimakawa irin wadannan yara da kudade da kuma ciyar da wasu.
Kungiyar CMAM na kula da yara da suka kai 46,107 amma a watan Disembar shekara ta 2016 yawan yaran ya karu zuwa 74,630 wanda hakan ya nuna cewa sama da kashi 70 bisa 100 na yaran dake fama da yunwa ba su sami tallafi na kirki a jihar ba.
Shugaban cibiyoyin kiwon lafiya ta jihar Jigawa Kabir Ibrahim yace saboda katutu da yunwa ta yi wa yara a jihar wanda hakan bai kamata ba ya sa wadansunsu basa iya kamala karatunsu.
Daga karshe Kabir ya yi kira ga attajiran jihar da su taimakawa talakawan jihar sannan su kirkiro shiryr-shirye da zai taimaka wajen kawar da matsalar yunwa da jihar ke fama da shi.