Kungiyan hadin kan kasashen Turai (EU) ta tallafawa ma’aikatan kiwon lafiyan ta Najeriya da kudade da ya kai yuro miliyan 70 domin kawar da cutar shan’i nna da kuma samar da ingantacciyar kiwon lafiya a kasa.
Jakadan kungiyan a kasa Najeria Michel Arrion yace dalilin yin hakan shine domin kananan yara da uwaye mata su sami ingantacciyar kiwon lafiya musamman ga talakawa da gyara cibiyoyin kiwon lafiya a wasu jihohi 5 da ke kasa Najeriya.
Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya jinjina wa kungiyar EU din sannan yace wannan tallafi zai taimaka wajen gyara cibiyoyin kiwon lafiya a kasa.
Ministan ya yi bayanin cewa za su yi amfanin da wasu daga cikin kudaden domin gyara asibitocin dake jihohin Adamawa, Bauchi, da jihar Kebbi