Bello ya auri Zainab a Jos

0

A ranar asabar da ya gabata ne Jarumi dan wasana fina-finan Hausa Bello Muhammed Bello ya auri masoyiyarsa Zainab a garin Jos jihar filato.

Wani cikin aminansa kuma abokin Bello, Hamisu Musa ya ce sun yi makaranta daya tare da Bello kuma kamar yadda ya sani Bello da Zainab sun kwashi tsawon shekaru da dama suna murza soyayya.

Ko da yake amarya Zainab ba yar wasan fina-finan Hausa bace shi Bello goga ne a harkar shirya fina-finai hausa.

Da yake masoyin kungiyar kwallon kafar Real Madrid ne sai da aka ware wata rana daya domin karrama wannan kungiya inda abokanansa suka sanya rigunan kungiyar kwallon kafar.

Ali Nuhu, Adam Zango, Sadiq Sani da sauransu duk sun hakarci taron bukin.

Share.

game da Author