Babban kotun dake sauraren karar tsohon gwamnan jihar katsina Ibrahim Shema ta ba da belin sa a zamanta da tayi yau Talata a Katsina.
Kotun ta ba da belin naira biliyan daya akansa da wadansu mutane uku da ake tuhuma da wawushe kudin jihar a lokacin da Shema yake gwamnan jihar da ya kai naira biliyan 11.
Alkali Ibrahim Bako da ya yanke hukuncin hakan a garin Katsina ya ce kotun tana da ikon sauraren wannan shari’a kuma tana da ikon yanke hukunci akai kamar yadda doka ta gindaya.
Ya yi watsi da korafin da Shema ya keyi cewa kotun bata da huruminta sauraren wannan kara sannan yace hukumar EFCC na da ikon tuhumar kowaye akan laifukan da ya shafi cin hanci da rashawa da yin sama da fadi da kudaden gwamnati.