Kungiyar kare hakkin musulmai (Muslim Rights Concern, MURIC) ta nuna goyon bayanta kan kiran da sarkin Kano Muhammadu Sanusi yayi na a kirkiro wata doka da zai hana duk wani na miji kara aure ba tare da ya cika wadansu sharudda ba kamar yadda addinin musulunci ya karantar.
Sarkin Kano Sanusi ya yi kira da kafa wata doka da zai rage yadda maza ke kara aure yadda suka dama ba tare da bin ka’idojin da addinin musulunci ya shimfida ba saboda kawai sun maida yin hakan wani abin jin dadi.
Darektan kungiyar Ishaq Akintola yace tabas wannan kira ya yi daidai domin haka Kur’ani mai girma ya karantar.
Ishaq ya fadi hakanne a garin Ibadan.
Ya ce kamar yadda bincike ya nuna, a zahiri mata sun fi maza yawa haka kuma Kur’ani mai girma ya ba namiji ikon iya auren mata 4 domin rage yawan mata wadanda basu da aure amma bai ce kuma ayi yadda zai zamo mana masifa a rayuwar ma’auratan da kasa ba.
Malam Ishaq ya kara bayanin cewa Kur’ani mai girma ya umurci namiji ya yi aure idan yana da abin da zai iya rike matan sa kuma zai iya kara wa idan yana da halin iya kula da su duka.
Daga karshe ya yabawa gwamnatin jihar Kano game da dokar da suke kokarin kafawa domin hakan kadai ne zai iya kare maza fadawa cikin matsalar auren matan da baza su iya kula da su ba da kuma haifo ‘ya’yan ba za su iya kula da sub a inda daga karshe su zamo bata gari.