Kakakin rundunar sojin Najeriya Janar SK Usman ya ziyarci PREMIUM TIMES

0

kakakin rundunar sojin Najeriya Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka ya ziyarci gidan jam’iyyar Premium Times a Abuja.

Janar Sani yace ya yi wannan ziyara ne domin jinjina ma gidan jaridar saboda kololiyar kwarewa da ta nuna a harkar aikin jarida.

Yace koda yake rundunar sojin ta dan sami rashin jituwa da gidan jaridar a wasu lokuta a baya yanzu sun yarda cewa tabbas akwai gidan jaridar da take da kima a idanuwar mutanen Najeriya.

Yace yayi farinciki da mamakin ganin irin kwararrun ma’aikata da suke aiki a gidan jarida da kuma gujema karban cin hanci da sukeyi.

Daga karshe ya ce abubuwan da suka faru a tsakaninsu da rundunar sojin sun faru ne saboda rashin fahimtar Juna musamman wajen samar da bayanai kan ayyukan sojin.

Shugaban gidan jaridar Premium Times Musikilu Mojeed ya gode wa rundunar sojin da Janar Sani kan irin wannan ziyara da ta kawo ma gidan jaridar sannan ya yi kira ga rundunar sojin da su hada hannu domin samun nasara musamman a yankin da sojojin Najeriya su keyi da Boko Haram.

Share.

game da Author