Shahararren mawakin nan Tuface Idibia ya ba da tallafin Miliyan uku da dubu dari biyar ga ‘yan gudun hijira.
Tuface ya ce yayi hakanne saboda halin da ya ga mazauna sansanin ‘yan gudun hijira din suke ciki.
Ya ce bayan ziyarar da ya kai wadansu sansanonin ‘yan gudun hijira dake yankin Arewa Maso Gabas abin baiyi masa dadi ba irin halin da ya gansu.
Ya mika cek din kudin ne ga hukumar majalisar dinkin duniya dake kula da ‘yan gudun hijira wato UNHCR, ya kuma ce gidauniyar sa na Tuface zata cigaba da yin aiki da kungiyoyin taimaka ma yan gudun hijira domin taimaka musu.
Hukumar ta gode wa mawakin sannan tace yayi wannan kyauta akan gaba domin UNHCR din na dan fama da rashin kudi saboda irin dawainiyan da suke tayi da yan gudun hijira din.