Dokar hana maza kara Aure: “Namiji ba dan goyo bane, abin da yake so kawai ya keyi – inji Matan Barno

3

Mata a jihar Borno sun fadi ra’ayin su akan Kiran da sarkin Kano Muhammadu Sanusi yayi na a kirkiro da wata doka da zai hana mazajen da basu da karfi auren mata da yawa.

Wasu daga cikin matan sun nuna goyon bayansu akan haka, wasu kuma sun ce hakan bai dace ba.

A makon da ya gabata ne Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya yi kira da a kirkiro da wata doka domin a hana mazajen da ba za su iya rike mata da ya wuce daya ba kara aure saboda barin su suna aikata hakan ya na sa da ga karshe dawainiyar ‘ya’yan yana komawa karkashin iyayensu mata.

Maimuna Garba, ta yi kira ga matan aure musamman na yankin arewa da su mara wa sarkin Kano baya akan wannan kudiri nasa.

“Ko me kace wa maza, koda karantarwa ce da ga Al’kur’ani maigirma ba za su yi amfani da shi sai wanda kawai suka ga yayi musu dadi shine zasu dauka.” Inji Maimuna.

Ita kuma Aisha Ibrahim, tace idan har kaga namiji na sauraron ka to kayi masa maganan Kara aure ne amma idan ba haka ba ba ma zai saurare ka ba.

“ Mafi yawancin maza suna sheke ayarsu a waje da wadansu matan bayan sun bar nasu a gida.” Aisha Tace.

Ta kara da yin kira ga maza da su bi karantarwar Al’kurani da bin sunnan manzon Allah (SAW) akan duk abin da za suyi da ya shafi musamman auratayya.

Ita kuma Amina Ba’ana, tace a nata fahimtar, Sarkin Kano bai yi kira da a hana maza kara aure ba. Tace abinda yake nufi shine maza su tabbatar da suna wadata iyalansu da abinci da ababan more rayuwa kamar yadda shari’a ta karantar.

Maryam Bala tace a nata ganin aure ba zabin mutum ba ne, zabin Allah ne, saboda yin hakan ba daidai bane.

“ Duk da cewa abubuwan da sarkin Kano ya fadi hakane amma a gaskiya hakan zai sa mata da yawa wadanda basuyi aure tukuna ba su shiga halin damuwa musamman ganin yadda maza ke dan tsada yanzu.”

Share.

game da Author