Muna murna da tsige Ali Ndume da majalisa tayi – Inji Jamiyyar APC

0

Jam’iyyar APC ta ce lallai tayi murna da tsige Ali Ndume da ‘ya’yan jam’iyyar suka yi yau a majalisar dattijai.

Kakakin Jam’iyyar Bolaji Abdullahi ne ya sanar da hakan ma wannan gidan jarida.

Ya ce dama can kokarin jam’iyyar shine a hado kan ‘ya’yan jam’iyyar a majalisar tun bayan rikicin shugabanci da ya faru a wancan lokacin.

Bolaji yace jam’iyyar tayi maraba da nadin Ahmed Lawan a matsayin shugaban masu rinjaye na majalisar.

Share.

game da Author