Sanata Ali Ndume ya ce dalilin da ya sa majalisa ta tsigeshi daga kujeran shugaban masu rinjaye bai wuce saboda tsayawa da yayi domin ganin majalisar ta amince da nadin Ibrahim Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC ba.
Ndume ya ce ziyarar da ya kai ma shugaban kasa da nuna kin amincewarsa da matsayin da majalisar ta dauka akan hakan ne ya sa shugabannin majalisar da na jam’iyyar APC a majalisar ta tsigeshi.
Jam’iyyar APC a majlisar ta amince da tsige shugaban masu rinjaye Ali Ndume da kuma musanyashi da Sanata Ahmed Lawan.
“Ko dayake kwanaki wani ya gayamini cewa wai Shugaban majalisar Bukola Saraki ya sa Sanata Dino Melaye ya nemi sanatoci su sa hannu domin a tsigeni amma duk ban dauka da gaske bane.
“Na dauka ay babu matsala asamu rashin jituwa tsakaninmu akan wani abu kawai sai ace wai an tsigeni.”