Kamfanin Sarrafa tumatirin gwangwani na Dangote za ta dawo aiki a watan Fabrairu

0

Babban darektan kamfanin sarrafa timatirin gwangwani na Dangote, Abdulkadir Kaita, yace idan Allah ya kaimu watan Fabrairun wannan shekara kamfanin zata dawo aikin sarafa tumatirin gwangwani gada gadan.

Kamfanin sarrafa tumatirin gwangwanin ya na garin Kadawa, karamar hukumar Kura, jihar Kano.

Ya ce dalilin dakatar da aiki a kamfanin a wancan lokacin shine domin karancin tumatir da aka samu ta dalilin cutar ‘Tuta Absoluta wanda yake rubar da tumatir tun da ga gona.

Jihohi biyar ne cutar tumatirin ya addaba a wancan shekaran wanda suka hada da jihohin Kaduna,Filato,Katsina da Jigawa.

Bayan haka ya kuma ce kamfanin na sa rai za’a samu wadataccen tumatir musamman daga manoman garuruwan Kadawa, Kura, Garun Malam da Hadeja-Jam’are wanda an sansu da noman timatir dinkuma hakan zai wadata kmfanin da isasshen tumatir domin sarrafawa.

Ya kuma yi bayanin cewa a rana kamfanin za ta iya sarafa tumatir din da ya kai tan 1,200.

Daga karshe ya ce duk da cewa sun dakatar da aikin a wancan shekaran kamfanin ta cigaba da biyan ma’aikatanta kuma idan tana neman Karin ma’aikata za ta sake dauka in Allah Ya yarda.

Karanta Labarin ta harshen turanci a nan: www.premiumtimesng.com

Share.

game da Author