Ba kamar yadda ake ta yadawa ba cewa wai zababben shugaban kasar Gambiya Adama Barrow ya rasu ba, PREMIUM TIMES ta wasu majiyoyinta masu karfi ta gano cewa Adama Barrow yana nan da ransa.
Majiyar na mu Jeffery Smith, ma’aikacin gidan jaridar Vanguard Africa da wani dan jaridar kasar Gambiya mai suna Demba Kandeh duk sun tabbatar mana da hakan.
Adama Barrow dai shine ya lashe zaben kasar Gambiya inda bayan amincewa da sakamakon zaben da shugaban kasar mai ci Yahya Jammeh ya yi kwatsam kuma sai ya dawo da baya ya ce bai yarda da sakamakon zaben ba saboda magudi da akayi.