Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu y ace shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi abin da tsohon Shugaban Goodluck Jonathan ya kasa yi a tsawon mulkinsa.
Tinubu ya fadi hakanne a jawabinsa a Kwalejin Tsaro da ke Abuja.
Tinubu ya jinjina ma sojojin Najeriya akan nasarorin da ta samu a yaki da Boko Haram.
Bayan haka kuma ya kara jinjin ma shugaban kasa akan rashin takura ma gidajen jaridu da gwamnatinsa ba sayi da kuma walwala da aka samu a harkar.
Daga karshe y ace jam’iyyar sa ta APC za ta cigaba da samar da ingantattun ayyuka domin mutanen Najeriya kamar yadda tayi alkawari.