Mun kusa shayo matsalar wutan lantarki a kasa Najeriya – Inji Fashola

2

Minsitan Ayukka, Wutan Lantarki da Gidaje Babatunde Fashola ya ce dalilin da ya sa kasa Najeriya ke ta fama da matsalar rashin wutan lantarki shine domin na’urorin da suke samarda wutan ba sa aiki yadda ya kamata soboda karancin iskar gas.

Ya kara da cewa na’urorin ya kamata su bada karfin wutan lantarkin da ya kai megawatts 3000 amma hakan bai yiwu ba wanda a dalilin hakan yasa idan aka sami wuta sai na’urorinn su kashe kansu.

Ya kuma ce hare-haren da kungiyar tsirarun Neja Delta suke kaiwa akan bututun man kasa yana daga cikin abubuwan dake kara kawo rashin wutan lantarkin kuma yana kara ruguza kokarin ma’aikatan nasa.

Bayan haka ministan ya ce suna yawan samin gobarar wuta a wuraren da ake samar da wutan lantarkin wanda idan hakan ya faru yakan sa a samu rashin wutan na dogon lokaci.

Fashola ya kawo misali da wata hadari da akayi na gobara da ta kama tashan Kainji da kuma tashan Afam wanda har yanzu ma’aikatar na kokarin ganin ta gyara kayan da suka kone a tashoshin.

Ministan yace yadda matakan gwamnati suke akan yadda ake biyan ‘yan kwangilan yakn sa ayyuka ya dade ba’a gama cikin lokaci ba domin aikin da ya kamata a gama shi a dan kankanin lokaci sai ya dauki tsawon lokaci ba’a yi shi ba.

Ministan ya ce kamfanonin da suke tatso mai wa gwamnatin Najeriya na bin gwamnatin bashi mai yawa kuma idan ba ta biya ba matsalar bata bututun mai da ‘yan tsirarun Neja-Delta ke yi ba zai daina ba.

Ya kuma ce biyan bashin zai taimaka wajen rage talauci wanda zai rage sata da ga yawancin ma’aikata kamfanonin.

Daga karshe Fashola yace saboda gyaran da suka da ge suna yi na’urorin na iya samarda wutan da ya kai megawatts 2900 kuma hakan zai taimaka wurin rage yawan dauke wutan da ake fama da shi a kasar kafin su gama gyaran da ya kamata.

Share.

game da Author