Mata na ta na lakadamini dukan tsiya saboda ta fi karfina – Lukman a kotu

1

Wani mutumi ya kai matarsa kotu saboda mai da shi jakan bugu da tayi a gidan aurensu.

Magidancin mai suna Lukman mazaunin jihar Ekiti ne.

Da yake sanar da kotu abinda mai dakinsa ta keyi masa yace duk lokacin da wani sabani ya hada shi da matarsa, ta kanyi masa dukan tsiya saboda ta fi shi karfi.

Lukman dai da matarsa Esther suna da yaya shida. Ya roki kotu da ta kashe auren domin ya gaji da shan duka.

Share.

game da Author