A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta a yanar gizo, an ga yadda wata ɗalibar makarantar masu kuɗi Leads dake Abuja, ta na gaggaura wa wata daliba mari yadda kasar uwarta saboda saurayi.
A bidiyon an ga yadda ɗalibar sanye da Inifom ta sharara wa wata ɗaliba dake tsaye a gabanta, sannan kuma wasu ɗaliba abokanta suna raha suna nishaɗi na jin daɗi.
Ita kuma wacce ake zabzabga wa mari ta na tsaye ta na kallonta har ta kai ta zauna amma ta cigaba da zabga mata mari.
Bayan Bidiyon y karaɗe shafukan yanar gizo sai iyaye suka ɗunguma makarantar domin jin dalilin yin sakaci ana barin ɗalibai na yin abu irin haka.
Daga baya dai makarantar ta bayyana cewa za abi diddigin maganar sannan kuma ɗalibar da ta rika yin mari ta fito a wani bidiyo tana rokon gafara.
Ta ce lallai ta yi nadamar abinda ta yi, kuma tana neman gafara, a yayyafe mata.
Discussion about this post