Ministocin Kiwon Lafiya na ƙasashen da zazzaɓin cizon sauro ya fi kashewa, sun ɗauki harama da ɗamarar kawo ƙarshen mugun kisan da cizon sauro ke yi a Afrika.
Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WHO), ya bayyana cewa kashi 95 bisa 100 na mutanen da ke mutuwa sanadiyyar zazzaɓin cizon sauro, duk a Afrika suke.
Haka WHO ta bayyana a taron ministocin ƙasashen da sauro ya fi yi wa illa a Yaounde, babban birnin ƙasar Kamaru.
WHO ta ce akwai ƙasashe 11 a Afirka, waɗanda nan ne ke da kashi 70 bisa 100 fama da zazzaɓin maleriya da kuma waɗanda cutar ke kashewa a duniya.
WHO ta bayyana cewa ƙasashen su ne Burkina Faso, Kamaru, Dimokraɗiyyar Jamhuriyar Kongo, Ghana, Mali, Mozambique, Nijar, Najeriya, Sudan, Uganda da Tanzaniya.
WHO ta ce tun daga 2017 shirin kakkaɓe zazzaɓin maleriya ke samun koma-baya a waɗannan ƙasashe, har zuwa yau.
Illar Zazzaɓin Cizon Sauro A Najeriya: Sauro Ya Kashe Mutum 190,000 A Najeriya – Ministan Lafiya:
Makonni biyu da suka gabata ne, Ministan Lafiya Muhammad Pate, ya bayyana cewa kashi 30 bisa 100 na matsalar zazzaɓin maleriya a duniya, duk a Najeriya ne ake fama da shi.
Ya ce sama da mutum miliyan 68 ne ya kamu da cutar zazzaɓin cizon sauro. Kuma ya ci rayuka 190,000.
Pate ya ce tun bayan ƙaddamar da yaƙi da zazzaɓin maleriya shekaru 70 da suka gabata, ya ci rayukan mutum 190,000 zuwa shekarar 2021.
Ministan Lafiya ya bayyana haka a shafin sa na Tiwita, wato X, bayan ganawar sa da CIbiyar Maleria Alliance, RBM Maleria Partnership da kuma Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WHO).
Ya ce an yi ganawar domin a sake tantance ƙoƙarin da ake yi ganin an kakkaɓe zazzaɓin maleriya a Najeriya.
Daga cikin abin da za a maida hankali inji ministan har da ƙoƙarin ganin maganin kashe sauro da kuma gidan sauro da kuma samar da magungunan zazzaɓi a ƙasar nan.
Pate ya ce akwai buƙatar amfani da sabbin dabarun da zasu iya yin aiki nagartacce a Najeriya da kuma Afirka.
Ya ce za a maida hankali “wajen gaggauta magance zazzaɓin maleriya musamman ga ƙananan yaran da suka kamu da kuma iyaye masu shayarwa da sauran su.”
Ya ƙara da cewa za a nunka yawan ƙananan cibiyoyin bayar da magani a matakin farko daga 8,800 da ake da su a ƙasar nan zuwa sama da 17,000.
Discussion about this post