Kwamishan ‘yan sandan jihar Anambra Aderemi Adeoye ya bayyana cewa dakarun ‘yan sandan jihar sun kama batagari 30 daga ranar 1 zuwa 30 ga Disemba 2023.
Adeoye ya fadi hara ranar Litini a taron da ya yi da manema labarai a Awka inda ya ke bayanin aiyukkan da rundunar ta yi a lokacin shagulgulan Kirismati.
Ya ce daga cikin wadanda da jami’an tsaron suka kama akwai mutum 12 da ake zargi da yin garkuwa da mutane, mutum 9 da laifin fashi da makami, 6 da laifin shiga kungiyar asiri da mutum uku da laifin ta’addanci.
Adeoye ya ce sun kama motocin 11, bindigogi 12, harsasai 40.
Bayan haka kwamishinan ‘yan sandan ya ce wasu ‘yan ta’adda sun kashe ‘yan sanda biyu dake aiki a jihar Enugu a karamar hukumar Aguata dake jihar Anambra.
Adeoye ya ce dakarun sun kama wadannan mutane a maboyar su dake dajin Igboji inda anan suka kashe mahara biyu.
Ya ce dakarun sun kama wani Emmanuel Orjiakor a Oba Wanda ya shahara wajen yin fashi da makami da yin garkuwa da mutane bayan ya samu rauni harsashi a dalilin batakashin da ya yi da ‘yan bangan jihar Anambra.
Adeoye ya ce dakarun sun kama Obinna Ekwunife mai shekara 27 bisa laifin yin garkuwa da wani Emmanuel Tobechukwu wanda ya kudin diyyarsa akan naira miliyan 9 ta POS.
“A ranar biyu da Disemba ‘yan sandan sun kama Olabo Ibrahim mai shekara 47 bisa laifin siyan mota kiran Lexus SUV na sata a Kwara dake Awka.
Discussion about this post