Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa ATBU dake jihar Bauchi ta dakatar da karatu na tsawon mako guda a dalilin zanga-zanga da ɗaliban jami’ar suka yi bayan kashe wani ɗalibin jami’ar da ƴan fashi suka yi.
Bisa ga sanarwar rufe jami’ar dake dauke da sa hannun mataimakiyar rajistarar makarantar Fatima Abdullahi wanda da ‘Daily Post’ ta gani ya nuna cewa Jami’ar ta dakatar da karatu daga ranar 4 zuwa 10 ga Disemba.
Jami’ar ta dauki wannan mataki domin guje wa matsalar karya doka a makarantar.
Jami’ar ta ce daga ranar Litini za ta dauki mataki mai tsauri kan duk dalibin da ta kama a harabar jami’ar.
Joseph Agabaidu wanda ke karantun kwas din ‘Applied Geology’ dake mataki na 500L ya gamu da ajalinsa ranar Asabar yayin da yake hanyarsa ta dawowa gidansa dake kasuwar Yelwan Tudu da misalin karfe bakwai na yamma.
Agabaidu ya rasu bayan ‘yan fashi sun daɓa masa wuka.
Ɗaliban jami’ar sun fusata ne ganin kamar ba a dauki wani mataki a kai ba.
Discussion about this post