Mutum 16 sun mutu wasu 27 sun ji rauni a hatsarin mota da ya auku a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Shugaban hukumar FRSC na jihar Kaduna Kabir Nadabo ya sanar da haka ranar Lahadi.
Nadabo ya ce hatsarin ya auku ranar Lahadi a dai-dai kauyen Audu Jangwon dake hanyar Kaduna zuwa Abuja da misalin karfe biyar da rabi na yamma.
Ya ce hatsarin ya auku yayin da wata babbar mota kirar DAF tirela mai lambar rajista KUJ 430XC ta kwace hanya ta fada wani kwari dake gefen titi.
“Binciken da rundunar ta gundar ya nuna cewa direban babban motan ya biyo hanyar da gudu baya ga yawan lodin kaya da ya yi inda a dalilin haka motar ta kwace masa.
Nadabo ya ce bayan ya isa wurin ya bada umarni kai wadanda suka ji rauni asibiti da kai matattun dakin ajiye gawa.
“Mun kuma janye motar da ta tare hanya sannan ma’aikatan mu sun ci gaba da gudanar da bincike.
Discussion about this post