Gwamnan Kaduna Uba Sani ya biya bashin tulin kudin wutar lantarkin Jami’ar KASU dake Kaduna na tun daga shekarar 2022 zuwa yanzu.
Wannan kokari na gwamna Uba zai sa a samu dawowar wutar lantarki a jami’ar da ke Kaduna da na Kafanchan, da suka dade suna fama da shi.
Bisa ga sanarwar da aka fitar dake dauke da sa hannun kakakin gwamnan Mohammed Shehu ya ce gwamnan ya biya bashin kudin wuta da jami’ar ke sha bayan da ya samu labarin rashin sa da jami’ar ke fama da tun a 2022.
“Bayan gwamnan ya samu labarin rashin wutan lantarkin da ake fama da shi a jami’ar ya umarci kwamishinan ilimi Muhammad Bello da ya gudanar da bincike domin kawo karshen matsalar.
Bayan haka sai gwamnati ta biya waɗannan bashin kuɗaɗe da ake bin jami’ar.
Gwamna Sani ya ce gwamnati za ta cigaba da kokarin kawar da matsalolin dalibai da malamai ke fama da su a jami’ar.
Wata dalibar jami’ar Amina Mohammed dake mataki na 300 ta ce rashin wutar lantarki a jami’ar ya sa daga gida take zuwa makaranta.
“Mafi yawan lokuta janareta ne ake amfani da shi sannan ko a hakan ma ba kowani lokaci ba.
Iyaye suma sun yaba da wannan huɓɓasa da gwamnan Sani ya yi game da matsalar wutar lantarki da jami’ar ke fama da shi.
Wani ma’aikacin kwalejin kimiya da fasaha ta Nuhu Bammali dake Zaria Usman Idris ya yi kira ga gwamnati da ta duba matsalar rashin wutan lantarki a Kwalejin.
Gwamnatin Kaduna ta ce harkar Ilimi na daga cikin abubuwan da wannan gwamnati za ta fi maida hankali akai.
Discussion about this post