Fitaccen kamfanin 24 Dot dake Kaduna, da ya shahara wajen aikin aikin talbijin da rediyo ya kirkiro shiri domin yi wa talakawan Najeriya musamman Arewa Iso ga gwamnati, wato mahukunta.
Wannan shiri mai suna ‘Tambarin Talaka’ ana nuna shi a shafukan sada zumunta dake yanar gizo, wato Intanet.
Da yake tattaunawa da wakiliyar PREMIUM TIMES HAUSA a Kaduna, shugaban kamfanin 24 Dot AbdulJabbar Ahmed, ya bayyana cewa wannan shiri zai rika yin bayani game da matsalolin da talaka fe fama da su a Najeriya.
” Mun lura cewa akwai matsaloli da dama da talakawan Najeriya ke fama da su. Waɗannan matsaloli sun haɗa da wasu ayyuka na gwamnati wanda ba su kaiwa ga Talaka da dai sauransu.
” A dalilin haka ne muka kirkiro wannan shiri domin mu yi wa talaka Iso ga gwamnati, ta ji irin matsalolin da suke fuskanta a rayuwa da zumman samun mafita.
Bayan haka shi kansa Jagoran shirin, Abdullahi Jibrin, wanda shine yake gabatar da shirin ya bayyana cewa, daga fara wannan shiri ya samu karbuwa matuka.
” Duk da dai mu baki ne har yanzu, alamu da muke gani ya nuna lallai muna samun karbuwa. Talaka na buƙatar a saurare shi, aji kukarsa don a share masa.
” Mun kirkiro wannan shiri ne domin Talaka. A rika yin fashin baki ga matsaloli, da wasu manufofin gwamnati, alfanunsu da rashin su. Inda za a gyara da inda za a maida hankali a kai.
“Tambarin Talaka, kamar yadda sunan yake, kamar kafa ce da za a rika tattauna batutuwan da suka shafi talaka da tsaretsaren gwamnati. A feɗe shi tun daga kai har wutsiya, sannan a bada shawarwari domin a samu gyara.
Wasu daga cikin masu kallon shirin da suka tattauna da PREMIUM TIMES HAUSA sun yaba wa kamfanin 24 Dot kan kirkiro shiri irin haka.
Mahmud Mohammed, ya ce ” Talaka ya dade ya na neman wuri irin haka da za a rika yi wa matsalolin sa da ayyukan gwamnati da fashin baki domin mahukunta su ji kuma su san dawan garin. Shune wannan shiri ya ɗore wadanda hakkin gyara ya rataya a kansu su gyara”.
Za ka kalli shirin Tambari Talaka a shafukan YouTube, Facebook da X
https://youtube.com/@Tambarintalaka?si=mM_Aks_u7syFQn6p
Discussion about this post