Shugaban Kasa Bola Tinubu ya gargadi jami’an gwamnati da su shiga taitayinsu tunda wuri, cewa kada wani ya rika leƙowa cikin zauren taro a fadar shugaban kasa a lokacin da ake mitin idan ba gayyatarsa aka yi ba.
” A makon jiya yayin da ake taron FEC a wannan zaure, na ga wasu sai su leƙo, wasu su fice daga zairen. Wasu ma har zama suke yi, ba a gayyace su ba kuma.
” Daga yau in so in ja muku kunne, ban yarda a rika haka ba a lokacin da muke mitin. Duk wanda ba a gayyace shi ba kada ya kuskura ya rika shigo mana wurin mitin.
“Waɗanda na amince musu su rika halartar zaman majalisar zartaswar a duk lokacin da za a yi sun haɗa da Hadiza Usman, mai ba da shawara ta musamman kan harkokin tsare-tsare da gudanarwa, Bayo Onanuga, mai ba da shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, Hakeem Muri-Okunola, babban sakatare mai zaman kansa da Damilotun Aderemi, sakatare mai zaman kanta.
” In banda waɗannan mutane, ba na su in ga wani da ba a gayyace shi ba yana leko mu a wannan zaure. Kuma nine da kaina zan ambaci sunansa idan muna buƙatar ya shigo cikin wurin taron.
Masu yin cecekuce kan shugaban maaikatana, Gbajabiamila, su shiga taitayinsu
Bayan haka Tinubu ya gargaɗi masu sukan shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila cewa su shiga taitayin su tunda wuri.
” Na yarda da aikinsa, masu yin cecekuce su ja bakin su su yi shiru. Ba zan amince da haka ba.
A ƙarshe Tinubu ya ce shi ba ma’asumi bane, zai iya yin kuskure. Amma kuma duk inda ya gano haka zai gyara.
Discussion about this post