A ƙoƙarin ta ga inganta karatun mata, Gwamnatin Jihar Bauchi za ta riƙa biyan mata ‘yan sakandare su 16,260 ladar Naira 5,000 da kuma Naira 10,000 a kowane zangon karatu.
Alawus na daga cikin Shirin Kwaɗaitar da Yara Mata Samun Ilmi wato AGILE.
Kwamishinar Ilmi wadda kuma ita ce Kodinetan Shirin AGILE, Jamila ce ta shaida wa manema labarai haka a ranar Asabar.
Ta ce gwamnatin Bauchi za ta riƙa biyan yara mata ‘yan ƙaramar sakandare Naira 5,000 duk kowane zangon karatu. Yayin da su kuma ‘yan babbar sakandare za a riƙa biyan su Naira 10,000 a kowane zango.
Jamila ta ce wannan shiri dai maƙasudin sa shi ne a bijiro da wasu hanyoyi daban waɗanda ba a taɓa gwadawa a baya ba, domin a inganta ilmi a Jihar Bauchi.
“Ana so a riƙa tallafa wa ɗaliban waɗanda suka daina zuwa makaranta, saboda matsalar tsadar rayuwa.” Inji ta.
“To waɗannan ɗalibai su na da damar sake komawa makaranta su ci gaba da karatun su har su kammala.
“An ƙirƙiro shirin ne hususan don yara mata ‘ya’yan marasa galihu, waɗanda ba su iya biya wa yaran su kuɗin kai su makaranta.
“Baya ganin an ƙara samun yawan ƙaruwar ɗalibai, shirin AGILE zai kuma tabbatar da cewa nagarta da ingancin ilmi na ƙaruwa sosai, ba raguwa ba.”
Discussion about this post