Asusun Kula da Al’amuran Yara Kanana na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta saka almajirai 20,800 cikin rajistar tsarin agaza wa marasa ƙarfi a jihar Katsina.
Shugaban aiyukka na musamman na SOCU Rabi Mohammed ta sanar da haka ranar Laraba a garin Katsina a zama da aka yi domin inganta al’umma.
Rabi ta ce an gudanar da wannan shiri a kananan hukumomi 3 dake jihar.
Ta ce an sa almajirai 5,882 a karamar hukumar Kafur, Mani 8,318 da Safana 6,106.
Shirin ya kuma yi wa almajirai 131 rajista daga jihohin Kaduna, Kano, Jigawa, Gombe, Bauchi, Zamfara da babban birnin tarayya Abuja.
Daga cikin yawan almajiran da aka yi wa rajista kashi 43.97% maza ne, kashi 56.3% mata.
“Daga cikinsu mun gano almajiran dake da nakasa, wadanda ke ciyar da kansu da wadanda malamansu ke ciyar da su.
“Mun Kuma gano wadanda ke da ilimin boko na JSE 1,397, masu ilimin makarantar firamare 6,311, masu ilimin SSE 221 sannan da wadanda basu da ilimin boko kwata-kwata 12,362.
“Shekarun almajiran ya fara daga masu shekaru 5-10 guda 8,208, masu shekara 11-15 sun kai 10,309, masu shekara 16-20 guda 1,671, da masu shekara 21-25 guda 103.
An kuma yi zama da masu ruwa da tsaki a fannin sannan an horas da wadanda za su nemi almajiran da za a saka a shirin.
Rabi ta ce da yawa daga cikin almajiran sun nuna rashin jin dadin su kan yadda iyayen su suka sake tituna suna barace barace da sunan wai suna karatu.
Discussion about this post