Gwamnatin Kaduna ta samar da motoci guda biyar da za a rika amfani da bin marasa lafiya har gida domin basu kula yadda ya kamata.
Waɗannan motoci za su rika shiga ƙauyuka suna bi kwararo kwararo, sako sako, lungu lungu domin kula da marasa lafiya a faɗin jihar.
Mataimakiyar gwamnan jihar KHadiza Balarabe ta sanar da haka a taron ci gaba da kaddamar da ayyukan da gwamna Uba Sani ya aiwatar cikin kwanaki 100 da darewar sa kujerar mulkin gwamnan Kaduna.
Hadiza ta ce gwamnati ta zuba ingantattun kayan aiki na zamani domin kula da lafiyar mutane musamman a kauyuka da wuraren dake da wahalan zuwa a jihar.
“Gwamnati ta yi haka ne domin farfado da fannin lafiyar jihar ta hanyar Samar da kwararrun ma’aikata, zuba ingantattun kayan aiki na zamani a asibitoci tare da gyara gine-ginen asibitocin domin mutanen jihar.
“Asibitin Tafi da Gidan ka zai rika yi wa mutane gwajin cututtuka da suka hada da cutar kanjamau, zazzabin cizon sauro, tarin fuka da sauran su sannan asibitin zai iya karabar haihuwa, yi wa mata awon ciki, bada magunguna da sauran su.
A nata jawabin kwamishinan lafiya Umma Ahmed ta ce wannan motoci za su rika yi wa mutane gwajin cututtuka kyauta.
Discussion about this post