Kotu a Karu dake Babban Birnin Tarayya, Abuja a ranar Litini ta tsare wasu matasa biyu bisa laifuffukan cin zarafi da sace kayan wani fasinja.
Rundunar ‘yan sanda ta kama Gabriel Samuel mai shekara 28 da Godswill Chigozie 25 duk mazauna Aso C, Mararaba, Nassarawa da laifin fashi da cin zarafin fasinjan.
Sai dai kuma Samuel da Chigozie sun musanta aikata laifin da ake zargin su da su.
Lauyan da ya shigar da karar Edwin Ochayi ya bayyana cewa wata fasinja Felicia Michael ‘yar jihar Nasarawa ta shiga motar haya daga Maitama zuwa titin Abacha tare da wadannan maza biyu inda yayin da suke cikin motan ne wadannan matasa suka nemi yi mata sata.
“Sai dai ita Felicia ta gane abinda waɗannan mutane suke so su yi mata sai ta ce wa direba ya tsaya za ta sauka amma ya ki tsayawa
“Zuwa can sai Ochayi ya ce sun kusa da gidan siyar da man fetur din AA.Rano inda a nan ne direban ya tsayar da motar.
“ Felicia ta ce daga man sai ɗaya daga cikin waɗannan mutane ya cire tabaron ta ya fasa sannan ya fizge jakanta da a ciki akwai katin ATM na bankin Stanbic, wayarta Samsung 5, wata waya karama, karamar waya da kudi naira 1,200.
Jami’an tsaro sun kama Samuel da Chigozie da wayar Nokia da kudi naira 1,200 sai dai kuma ɓarayin ba su iya faɗin yadda suka yi da wayar Samsung ɗin ba.
Alkalin kotun Umar Mayana ya ce kowanen su zai biya kudin belin Naira 100,000 sannan kowannen su zai gabatar da shaida daya dake zama a wurin da kotun ke da iko.
Za a ci gaba da shari’ar ranar 17 ga Yuli.
Discussion about this post