A majalisar jihar Kaduna, Yusuf Liman ne ya zama kakakin majalisar jihar Kaduna yayin da Magaji Henry ya zama mataikain Kakakin majalisa.
Dan takara ɗaya tilo wanda ya tsaya, kuma tsohon kakakin majalisar, Yusuf Zailani ya janye daga takarar kafin akai ga yin zaɓe.
Bayan haka gwamnan Kaduna, Uba Sani ya aika da sakon taya murna ga sabbin shugabannin majalisar, yana mai fatan Allah ya basu damar yin aiki tare cikin aminci da lumana domin cigaban mutanen jihar Kaduna.
Discussion about this post